logo

HAUSA

Rahoto: Tasirin da takunkuman da Amurka ta sanyawa Xinjiang zai haifar ga kamfanonin auduga na duniya

2021-12-26 20:22:23 CRI

Rahoto: Tasirin da takunkuman da Amurka ta sanyawa Xinjiang zai haifar ga kamfanonin auduga na duniya_fororder_auduga

A shekarun baya bayan nan, kasar Amurka ta sanya takunkumai kan audugar da ake samarwa a yankin Xinjiang na kasar Sin, karkashin abin da Amurkar ta kira da sunan “aikin tilas” da “take hakkin dan adam”, matakin da ya yi mummunar illa tare da lalata audugar dake samarwa a Xinjiang, har ma ta yi kokarin janyo hankalin wasu kamfanoni da dama kan su kauracewa audugar Xinjiang.

Domin fahimtar irin tasirin da takunkumin Amurkar ya yi kan batun dake shafar yankin Xinjiang ga hada hadar cinikayyar kamfanonin auduga na kasa da kasa, da kuma kamfanin audugar kasar Sin, wata tawagar masu bincike daga jami’ar Jinan ta kasar Sin ta kammala wani bincike mai zaman kansa, inda ta fidda rahoto mai taken “tasirin takunkuman da Amurka ta azawa Xinjiang zai haifar ga tsarin cinikayyar kamfanonin auduga na kasa da kasa" ta hanyar binciken bin diddigi wajen ziyartar wurare, tare da yin nazari, an fidda rahoton a yau 26 ga wata.

Rahoton ya bayyana cewa, takunkuman da Amurkar ta aza bisa moriyar siyasar bangaranci sun lalata harkokin hada hadar kamfanonin auduga na kasa da kasa, kuma batun da ake kira da sunan “aikin tilas” da “take hakkin dan adam" wasu kalamai ne da Amurkar ke amfani da su don yadawa sauran kasashen duniya, da nufin kara yin tasiri wajen yin mulkin kama karya.(Ahmad)