logo

HAUSA

An gudanar da taron bidiyo domin bayyanawa baki ’yan Senegal labaran jihar Xinjiang

2021-12-24 10:00:12 CRI

An gudanar da taron bidiyo domin bayyanawa baki ’yan Senegal labaran jihar Xinjiang_fororder_211224-F1-Xinjiang

Gwamnatin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta dake arewa maso yammacin kasar Sin da ofishin jakadancin Sin a Senegal, sun gudanar da wani taro ta kafar bidiyo a jiya Alhamis, da nufin bayyana yanayin da jihar take ciki a yanzu ga baki ’yan kasar Senegal.

Sama da mutane 20 da suka hada da jami’an gwmanati da masana da ’yan jarida da dalibai daga kasashen Afrika ne suka halarci taron ta kafar intanet.

Bayan sauraron labarai da tattaunawa da ’yan asalin jihar, mahalarta taron sun fahimci yanayin zamantakewar jama’ar jihar da ci gaban tattalin arzikinta da ’yancin bin addini da ingantuwar da rayuwar jama’a ta samu.

Jakadan Sin a Senegal, Xiao Han ya ce, dubban jami’an diflomasiyya da yan jarida da shugabannin addinai daga kasashe sama da 100 ne suka ziyarci Xinjiang a shekarun baya-bayan nan, sannan kuma ana maraba da mahalarta wannan taro su ziyarci jihar domin ganewa idanunsu.

A nasu bangaren, bakin na kasar Senegal, sun ce karin musaya irin wannan za ta taimakawa al’ummar kasarsu kyautata fahimtarsu game da ainihin yanayin jihar Xinjiang. (Fa’iza Mustapha)