logo

HAUSA

Majalisar ministocin Masar ta yi taronta na farko a sabon babban birnin kasar

2021-12-24 10:34:56 CRI

Majalisar ministocin Masar ta yi taronta na farko a sabon babban birnin kasar_fororder_211224-I3-Masar

Jiya ne, majalisar ministocin kasar Masar, ta gudanar da taronta na farko a sabon babban birnin kasar, a wani bangare na shirin gwamnatin kasar na komawa babban birnin kasar nan da karshen watan Disamba.

Gwamnatin Masar ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, taron ya tattauna batutuwan siyasa, da zamantakewa da tattalin arziki, da kuma sabbin ci gaban da aka samu game da COVID-19, da yadda za a samar da alluran rigakafin cutar ga 'yan kasar.

Firaministan Masar Mostafa Madbouli ya ce, taron na jiya, wani sako ne mai karfi da kasar ta aikewa duniya cewa, Masar ta kama hanyar kaiwa ga samun makoma mai kyau, duk da kalubalen da ake fuskanta.

A watan Nuwamba ne, shugaba Abdel Fattah Al-Sisi, ya umurci gwamnati da ta fara mayar da ma'aikatan gwamnati zuwa gundumar gwamnati dake sabon babban birnin kasar na tsawon watanni 6 na gwaji daga watan Disamba. (Ibrahim Yaya)