logo

HAUSA

CMG ya gabatar da manyan labaran tattalin arzikin duniya guda goma na shekarar 2021

2021-12-24 16:33:18 CRI

CMG ya gabatar da manyan labaran tattalin arzikin duniya guda goma na shekarar 2021_fororder_hoto

Kwanan baya, babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya gabatar da manyan labarai na tattalin arzikin duniya guda 10 na shekarar 2021.

Wadannan labarai guda goma sun hada da:

  1. Kasar Sin ta cika shekaru 20 da shiga kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO.
  2. An bude layin dogo a tsakanin kasar Sin da kasar Laos.
  3. An cimma matsaya kan yadda za a aiwatar da “Yarjejeniyar Paris” a taron sauyin yanayi na birnin Grasse na kasar Faransa.
  4. Kasashe da dama suna fuskantar kalubale a fannin tsarin samar da kayayyaki tsakanin kasa da kasa, sakamakon yaduwar annobar cutar COVID-19.
  5. Farashin kayayyaki ya yi tashin da ba a taba ganin irinsa ba cikin shekaru 40 a kasar Amurka.
  6. Farashin abinci ya yi karuwar da ba a taba ganin irinsa ba cikin shekaru 10 a kasashen duniya.
  7. Kasashe da dama sun yi gargadin karancin makamashi sakamakon rashin daidaito a tsakanin yawan makamashi da aka samar da bukatun jama’a.
  8. Rundunar sojojin kasar Amurka ta kashe dallar Amurka sama da triliyan 2 cikin shekaru 20 da suka gabata, sakamakon matakan soja da ta dauka a kasar Afghanistan.
  9. Kasuwannin sarrafa da sayar da motoci masu amfani da wutar lantarki suna karuwa da habaka cikin sauri.
  10.  Zirga-zirgar sararin samaniya na kasuwanci ta fara samun karbuwa. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)