logo

HAUSA

'Yan sandan Najeriya sun ceto mutane 48 da aka sace a yankin arewacin kasar

2021-12-24 09:48:14 CRI

Rundunar ’yan sandan Najeriya ta ce, jami’anta sun yi nasarar ceto mutane 48 nan take, bayan da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su, a wata babbar hanya a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya a ranar Laraba.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Kaduna Mohammed Jalige ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa, wasu ’yan bindiga da dama ne suka kai wa ayarin motocin ’yan kasuwa da ’yan sanda ke yi musu rakiya hari a ranar Laraba da safe, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa birnin Kaduna, babban birnin jihar. Inda ’yan bindigar suka yi awon gaba da ’yan kasuwar masu tarin yawa zuwa dajin da ke kusa bayan harin na ba-zata.

Sai dai Jalige ya ce, ’yan sanda dake yiwa ’yan kasuwar rakiya sun karfafa kan su, inda suka tunkari ’yan bindigar cikin dabara, domin kada su cutar da wadanda abin ya shafa.

A halin da ake ciki, ana ci gaba da kokarin ganin an kubutar da dan kasuwar da ya bace cikin koshin lafiya, yayin da za a kara samar da karin ma’aikata domin karfafa tsaro a yankin. (Ibrahim Yaya)