logo

HAUSA

An kaddamar da taron tattaunawa kan yaki da ta’addanci na kasa da kasa karo na biyu

2021-12-23 11:16:44 CRI

An kaddamar da taron tattaunawa kan yaki da ta’addanci na kasa da kasa karo na biyu_fororder_W020211223340204503733

An kaddamar da taron tattaunawa kan yaki da ta’addanci na kasa da kasa karo na biyu a nan birnin Beijing jiya Laraba bisa taken “Sabon yanayi da sabbin barazana da kalubalolin da ake fuskanta a yaki da ta’ddanci da sabbin matakan da za a dauka”. Ayyukan ta’addanci na kara tsananta, saboda yadda masu aikata laifin ke amfani da dabaru na kimiyya da fasaha, lamarin da ya haifar da sabbin kalubaloli da barazana ga al’ummar duniya. Don haka, mahalartan taron suka bayyana cewa, dole ne kasashen duniya su kara hada kai don kawo karshen wannan matsala

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Wu Jianghao ya bayyana a gun taron cewa, a duk lokacin da ake fuskantar ta’addanci maras iyaka, ya kamata a tsaya tsayin daka wajen tabbatar da tsaron duniya bai daya, da hada kai, da dorewar zaman lafiya, da ci gaba da karfafa shawarwari, da hadin gwiwa kan yaki da ta’addanci na kasa da kasa, da shiga tsakani, don mayar da martani da sabbin barazana da kalubaloli.

Mukadashin darektan cibiyar bincike kan yaki da ta’addanci ta AU Idriss Mounir Lallali ya nuna cewa, hadin kan shiyya-shiyya da kasa da kasa na taka muhimmiyar rawa wajen yaki da ta’addanci. A sa’i daya kuma, akwai bukatar kawar da ta’ddanci daga tushe. (Amina Xu)