logo

HAUSA

Najeriya ta lalata alluran rigakafin COVID-19 miliyan 1 da suka lalace

2021-12-23 09:23:03 CRI

Najeriya ta lalata alluran rigakafin COVID-19 miliyan 1 da suka lalace_fororder_11

A ranar Laraba gwamnatin Najeriya ta lalata alluran rigakafin COVID-19 sama da miliyan daya wadanda aka tattaro daga sassan kasar bayan da aka gano wa’adin amfani da su ya kusa karewa.

Hukumar bunkasa kiwon lafiyar al’umma a matakin farko ta kasa  (NPHCDA), wacce ke jagorantar aikin riga-kafi a kasar, da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasar NAFDAC ne suka jagoranci aiki lalata alluran a wajen tara shara dake Abuja, babban birnin kasar.

Faisal Shuaib, shugaban hukumar NPHCDA, ya bayyanawa manema labarai a wajen lalata alluran cewa, kasar mafi yawan al’umma a Afrika ta yanke wannan shawara ne don bin sahun sauran kasashen Afrika wadanda su ma sun riga sun lalata rigakafin COVID-19 saboda dalili iri daya, matakin zai karawa ‘yan Najeriya kwarin gwiwa game da shirin rigakafin da ake gudanarwa a kasar.

Jami’in ya ce, sun kwashe alluran rigakafin kimanin 1,066,214, wadanda wa’adin amfaninsu ya kare na kamfanin AstraZeneca a duk fadin kasar, ya ce mai yiwuwa ne alluran suna da karfi gabanin hukumomin lafiyar Najeriyar su dauki wannan mataki na kwashe su.(Ahmad)