logo

HAUSA

Wani rahoto ya fallasa gazawa da koma baya na dimokuradiyyar Amurka

2021-12-23 13:39:01 CRI

Kungiyar nazarin hakkin dan Adam ta kasar Sin, jiya Laraba ta fitar da wani rahoto, inda ya bayyana gazawa da kuma koma baya ga demokiradiyyar Amurka.

Rahoton ya ce, tsarin demokuradiyyar Amurka wanda ya ta’allaka ta hanyar jefa kuri'a don gudanar da zabuka, ba zai iya kaiwa ga dorewar cikakkiyar ma’anar siyasar demokuradiyya ba, kuma hakan bai zama kyakkyawan tsari ga demokuradiyya ta zamani ba.

Haka kuma, rahoton ya yi bayani kan halaye na siyasa, da gazawar tarihi, da kuma koma baya na demokuradiyyar Amurka, wanda ya nuna cewa, Amurka ta dade tana tauye wa wadanda ba fararen fata ba, ‘yancinsu na shiga a dama da su a harkoki na demokuradiyya, ta hanyar yi musu kora da hali, da mayar da su saniyar ware, da kuma hadewa da Indiyawan daji na dogon lokaci. Baya ga yadda, Amurka ta dade tana tauye hakkin mata na zabe kan takwarorinsu maza.

Har ila yau, rahoton ya fallasa yadda tsarin mulkin demokuradiyyar Amurka ya raba kan ‘yan kasa, da amfani da ma'auni biyu, da yadda kudi ke yin tasiri da kuma yadda aka gina tsarin demokiradiyar ta Amurka.(Ibrahim)