logo

HAUSA

Jami’in WHO ya yi gargadi kan shirin rigakafi mai kara karfin garkuwar jiki zai tsawaita annoba COVID-19

2021-12-23 10:34:02 CRI

Jami’in WHO ya yi gargadi kan shirin rigakafi mai kara karfin garkuwar jiki zai tsawaita annoba COVID-19_fororder_88

Babban jami’in hukumar lafiya ta duniya WHO, ya yi gargadin cewa bullo da shirye-shiryen gudanar da rigakafin kara karfin garkuwar jiki na bai daya zai iya tsawaita annobar COVID-19 maimakon kawo karshen cutar, sakamakon rashin daidaito na rarraba rigakafin a tsakanin kasashe masu sukuni da matalauta.

Darakta janar na hukumar WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya fadawa taron manema labarai cewa, rashin samar da rigakafin ga kasashen dake tsananin bukatarsa zai baiwa kwayar cutar karin damammakin ci gaba da yaduwa da kuma sauya kamannin cutar.

Tedros ya ce, hukumar WHO ta sha yin kira ga kasashen duniya da su yi kokarin cimma kashi 40 bisa 100 na alluran rigakafin ga al’ummar kasashensu kafin karshen wannan shekarar, to sai dai rabin kasashen mambobin WHO ne suka cimma nasara kaiwa adadin, wanda hakan ya yi matukar haifar da rashin daidaito a tsarin rarraba alluran rigakafin a duniya.

Yayin da wasu kasashen ke gudanar da shirin bai daya na rigakafin mai kara karfin garkuwar jiki, mutane uku cikin hudu na ma’aikatan lafiya a Afrika har yanzu ba su samu yin rigakafin ba ya zuwa karshen shekarar 2021, wato shekara guda tun bayan karbar zagayen farko na rigakafin.(Ahmad)