logo

HAUSA

Kasar Sin na kara samun ci gaba mai dorewa

2021-12-22 13:37:09 CRI

Kasar Sin na kara samun ci gaba mai dorewa_fororder_1

Jiya Talata aka fitar da wani rahoton dake nazarin ci gaban kasar Sin mai dorewa na shekarar da muke ciki, inda ya shaida cewa, kasar na kara samun ci gaba mai dorewa. Kana rahoton ya ba da shawarwari guda biyar don inganta irin wannan ci gaban.

Rahoton ya nuna cewa, daga shekara ta 2015 zuwa 2019, tattalin arziki gami da rayuwar al’ummar kasar Sin sun ci gaba da kyautata, kana, an samu manyan nasarori a fannonin kyautata yanayin zuba jari, da kiyaye muhallin halittu da sauransu. Shehun malami a jami’ar Columbia dake Amurka, Shi Tianjie ya bayyana cewa, baya ga ci gaban tattalin arziki, akwai wasu shaidun dake tabbatar da cewa, kasar Sin na kara samun ci gaba mai dorewa.

Rahoton ya kuma ba da shawarwari a wasu muhimman fannoni biyar, kan yadda za a inganta samar da ci gaba mai dorewa a kasar Sin, ciki har da tabbatar da nasarorin da aka samu wajen kawar da talauci, da jagorantar aikin sauya salon sana’o’i ta hanyar kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da kara kyautata muhallin halittu, da inganta lafiyar dan Adam, tare kuma da kara taka rawa a fadin duniya. (Murtala Zhang)