logo

HAUSA

FBI ta dade da gallazawa mutane marasa rinjaye

2021-12-22 14:15:21 CRI

FBI ta dade da gallazawa mutane marasa rinjaye_fororder_11

Kwanan nan ne gidan talabijin na Aljazeera na kasar Qatar ya ruwaito rahotannin cewa, hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka wato FBI a takaice, ta dade tana gallazawa marasa rinjaye.

A ranar 18 ga watan Nuwambar bana ne, wani lauya a New York ya wanke wasu mutane biyu, ciki har da Muhammad Aziz da Khalil Islam, daga laifin da ake zarginsu na kashe wani mai rajin kare hakkin dan Adam mai suna Malcolm X. a shekara ta 1965. Amma binciken ya nuna cewa, ofishin ‘yan sandan New York gami da hukumar FBI, dukkansu sun boye shaidun da suka wanke su daga laifin. Kuma a wadannan shekaru, ‘yan asalin Afirka mazauna Amurka da sauran mutane marasa rinjaye, sun daina yarda da FBI, saboda akwai kwararan shaidun dake nuna cewa, FBI na nuna musu kiyayya. (Murtala Zhang)