logo

HAUSA

Rahoto: Tattalin arzikin Sin ya samar da karin damar hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasa da kasa

2021-12-22 10:07:11 CRI

Rahoto: Tattalin arzikin Sin ya samar da karin damar hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasa da kasa_fororder_sin

Jiya ne, cibiyar nazarin harkokin duniya, ta fitar da wani rahoto mai taken "Hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya ta kasa da kasa ta kasar Sin karkashin sabon tsarin raya kasa" a nan birnin Beijing. Rahoton ya nuna cewa, akwai kyakkyawan makoma na samun hadin gwiwa a duniya a fannin tattalin arziki na zamani, da tattalin arziki maras gurbata muhalli, da gina ababen more rayuwa, da cinikayyar hidimomi. A sa'i daya kuma, tattalin arzikin kasar Sin ya kara samar da zarafi ga hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasa da kasa.

A gabatarwarsa, rahoton ya mayar da hankali ne kan hadin gwiwar kasa da kasa a fannin tattalin arziki, da cinikayya na kasar Sin, kuma ya yi nazari kan fannoni daban-daban a dukkan matakai. Rahoton ya kuma gabatar da sabbin dabaru, da damammaki na hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da kasashen waje a nan gaba. A sa'i daya kuma, ya gabatar da shawarwari masu ma'ana, kan yadda kasar Sin za ta shiga zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya ta kasa da kasa bisa yanayi na hangen nesa yadda ya kamata.(Ibrahim)