logo

HAUSA

Wakilin Sin ya nuna damuwa kan yanayin tsaro a yankin Falasdinu da aka mamaye

2021-12-22 09:59:33 CRI

Wakilin kasar Sin a MDD, ya bayyana damuwarsa kan halin tsaro da ake ciki a yankin Falasdinu da aka mamaye, ya kuma yi kira ga bangarori da su kai zuciya nesa.

Jami’in na Sin ya fadawa kwamitin sulhun majalisar cewa, kamata ya yi Isra’ila ta cika alkawarinta karkashin dokar jin kai ta kasa da kasa, ta tabbatar da tsaro ga al’ummar yankin da ta mamaye da dukiyoyinsu, ta kuma yi nazari sosai kan hare-haren da ake kaiwa matsugunan, da kuma abubuwan da suka faru na cin zarafin jama’a, a kuma gurfanar da masu laifi a gaban kotu. A sa'i daya kuma, wakilin na kasar Sin cewa ya yi, ya kamata a mutunta 'yancin wanzuwar Isra'ila da kuma matsalolin tsaron da ke damunta.

Kasar Sin ta yi kira ga kasashen duniya, da su kara kokarin da suke yi na samar da zaman lafiya. Haka kuma kasar Sin tana goyon bayan MDD, da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa, da kungiyar hadin kan kasashen musulmi, da kuma kasashen da ke da gagarumin tasiri wajen taka muhimmiyar rawa a wannan batu.(Ibrahim)