logo

HAUSA

Kwamitin sulhun MDD ya kara tsawaita wa’adin tawagar wanzar da zaman lafiya ta AU a Somaliya

2021-12-22 10:12:27 CRI

A jiya Talata kwamitin sulhun MDD ya amince da kudirin sake tsawaita wa’adin aikin dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika AU da aka tura Somaliya da karin watanni uku, har zuwa ranar 31 ga watan Maris na 2022.

Kudirin mai lamba 2614, wanda ya samu amincewar dukkan mambobin kwamitin sulhun 15, ya amince tawagar wanzar da zaman lafiyar ta kungiyar AU dake Somaliya wato AMISOM, ta ci gaba da daukar dukkan matakan da suka dace, tare da mutunta cikakken ‘yancin yankunan kasa, da kiyaye yankunan kasar, da kaucewa shigar harkokin siyasa, da tabbatar da hadin kan al’ummar Somaliya, yayin da suke gudanar da ayyukansu a wannan karo.

An dorawa tawagar AMISOM alhakin kawar da barazanar da kungiyar al-Shabaab da sauran kungiyoyi masu dauke da makamai ke haifarwa ga zaman lafiyar kasar Somaliya.

Kungiyar tarayyar Afrika AU ta kafa AMISOM a watan Janairun 2007. Ayyukanta sun samu amincewar kwamitin sulhunn MDD.(Ahmad)