logo

HAUSA

Zimbabwe ta karbi sabon tallafin alluran rigakafin COVID-19 daga Sin

2021-12-21 09:24:18 CRI

Zimbabwe ta karbi sabon tallafin alluran rigakafin COVID-19 daga Sin_fororder_zimbabwe

Jiya ne, kasar Zimbabwe ta karbi wani rukunin alluran rigakafin COVID-19 na kamfanin Sinovac daga kasar Sin, wanda ake fatan zai kara karfin shirin kasar na yiwa al’ummunta rigakafin cutar, a yayin da take fama da bullar annobar COVID-19 zagaye na hudu.

Gudunmawar ta baya-bayan nan, da ma wasu rukunin rigakafin da kasar Sin ta riga ta baiwa kasar ta Zimbabwe, ya biyo bayan alkawarin da kasar Sin ta yi ne a taron ministoci karo na takwas, na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC), na samar da karin alluran rigakafin COVID-19 biliyan 1 ga Afirka. Wannan adadin, ya hada da allurai miliyan 600 a matsayin gudummawa, da kuma wasu alluran miliyan 400, da za a samarwa kasashen na Afirka, ta hanyoyin hadin gwiwa da kamfanonin kasar Sin da kasashen Afirka da abin ya shafa ke samarwa.

Da yake jawabi jim kadan bayan karbar tallafin a filin jirgin sama na Robert Gabriel Mugabe da ke birnin Harare, babban birnin kasar, mataimakin shugaban kasar Zimbabwe, kana ministan kiwon lafiya na kasar, Constantino Chiwenga, ya bayyana jin dadinsa da alluran da kasar Sin ta samarwa kasarsa, yana mai cewa, tallafin zai taimaka wajen gaggauta aikin rigakafin a Zimbabwe.

Chiwenga ya ce, kasashen Zimbabwe da Sin na da kyakkyawar alaka, kamar yadda ake iya gani a hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu bisa manyan tsare-tsare a sassa da dama na tattalin arziki.

A nasa jawabi a wajen taron, jakadan kasar Sin dake Zimbabwe, Guo Shaochun, ya jaddada aniyar kasar Sin ta taimakawa kasashen Afirka wajen yaki da COVID-19, da kuma magance matsalar rashin daidaiton alluran rigakafi.(Ibrahim)