logo

HAUSA

An Kaddamar Da "Rahoton Alkaluman Ci gaban Matasa Na Kasa Da Kasa Na 2021"

2021-12-21 13:45:55 cri

An Kaddamar Da "Rahoton Alkaluman Ci gaban Matasa Na Kasa Da Kasa Na 2021"_fororder_04C7AB54CD3C4BEBA9D46722C1D6BABCD64ABEBB_size101_w1024_h683

A yayin taron dandalin tattaunawar ci gaban matasan kasar Sin karo na 17 da aka gudanar a ranar 18 ga wata, an fitar da "Rahoton alkaluman ci gaban matasa na kasa da kasa na shekarar 2021", wanda ya nuna halin da ci gaban matasan kasashe daban daban ke ciki, da halin musamman da kuma matsalolin da suke fuskanta.

Bisa la’akari da fannonin dake jawo hankulan galibin matasan kasashe daban daban, ciki har da ilimi, kiwon lafiya, auratayya, samu aikin yi da raya sana’o’i, cudanya da jama’a da kuma kare hakkoki da dai sauransu, rahoton ya zabi kasashe 85 domin aunawa tare da gabatar da wani cikakken yanayi game da ci gaban matasa a kasashe daban-daban.

Rahoton ya kuma nuna cewa, matsayin ci gaban matasa a kasashe daban daban ya karu matuka a 'yan shekarun nan. Kasashe daban daban suna ba da muhimmanci ga batun samar da ayyukan yi ga matasa, da daukar matakai daban daban na kara samar da cikakken aikin yi ga matasa, da kokarin inganta shigar da matasa cikin harkokin al’umma da kuma cimma nasara wasu sakamako. (Mai fassara: Bilkisu Xin)