logo

HAUSA

Jami'in MDD ya yi Allah wadai da harin da aka kai kan ma'aikacin jin kai a Sudan ta Kudu

2021-12-21 10:12:34 CRI

Mukaddashin jami’in tsare-tsaren ayyukan jin kai na MDD a Sudan ta Kudu Mathew Hollingworth, ya yi Allah wadai da harin da aka kai, kan ayarin motocin shirin samar da abinci na MDD (WFP), da ma kisan wani ma'aikacin jin kai dake yiwa majalisar aiki tare da jikkata wani.

Mathew Hollingworth ya ce, wasu mutane dauke da makamai ne, suka kai hari a ranar Lahadin da ta gabata ga ayarin motocin dakon kaya guda biyar na shirin, tsakanin Tindiir da kauyen Duk Padiet na jihar Jonglei, a yankin arewa maso yammacin kasar, inda suka yiwa motocin ruwan harsasai.

Hollingworth ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a Juba, babban birnin kasar cewa, kowane ma'aikacin jin kai a kasar ta Sudan ta kudu, yana da 'yancin gudanar da aikinsa cikin yanayi na tsaro da kwanciyar hankali.

Jami’in ya ce, tawagar na dawowa ne daga Tindiir, inda suka kai agajin abinci mai muhimmanci na ceto rai, ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa, yayin da aka yi musu kwanton bauna.

Ya ce, hakika wadannan motocin aka nufa. Dole ne in yarda cewa, wannan hari ne da aka shirya, kuma ya saba wa dokar ba da agaji ta duniya. Dole ne a daina wannan danyen aiki.(Ibrahim)