logo

HAUSA

Kasar Sin ta kafa cibiyar kula da iskar gas

2021-12-21 09:38:28 CRI

Kasar Sin ta kafa cibiyar kula da iskar gas_fororder_iska

Hukumar kula da yanayi ta kasar Sin ta bayyana cewa, kasar ta kafa cibiyar kula da iskar gas ta farko bayan shafe kusan shekaru 40 ana aikin gina ta.

Wannan sanarwar na zuwa ne, bayan da hukumar ta fitar da kundin tarihin sa ido kan iskar gas na farko na kasa, wanda ya kunshi manyan tashoshin sa ido guda 60 da ke kunshe da muhimman wurare masu matukar muhimmanci a kasar.

Abubuwan da ake sanya ido, sun kunshi nau'o’in iskar gas guda bakwai da aka kayyade a cikin yarjejeniyar Kyoto, gami da carbon dioxide, methane da nitrous oxide.

Kasar Sin dai na daya daga cikin kasashen duniya na farko, da suka gudanar da aikin lura da iskar gas a baya. A shekarar 1982 ne, aka fara amfani da tashar sa ido kan yanayin na farko na kasar Sin a birnin Beijing, fadar mulkin kasar.

Wani babban jami'i a hukumar Cao Xiaozhong, ya danganta kafa cibiyar da yadda kasar Sin ke ci gaba da shiga cikin shirin kula da yanayin duniya na hukumar hasashen yanayi ta duniya.(Ibrahim)