logo

HAUSA

An zabi dukkan mambobi 90 na majalisar tsara dokokin HK ta bakwai

2021-12-20 14:37:52 CRI

An zabi dukkan mambobi 90 na majalisar tsara dokokin HK ta bakwai_fororder_zabe

Ya zuwa safiyar Litinin din an kammala zabar dukkan mambobi 90 na majalisar tsara dokoki ta bakwai ta yankin musamman na Hong Kong.

Kwamitin gudanar da zaben ya zabi mambobin, bayan da masu zabe sama da miliyan 1.35 suka jefa kuri’unsu a ranar Lahadi.

Ofishin cudanya na gwamnatin tsakiya ta kasar Sin dake Hong Kong, a yau Litinin ya yaba da nasarar da aka samu na kammala zaben, a sanarwa da ya fitar ta kafar intanet bayan bayyana sakamakon zaben.

Ofishin ya bayyana zaben a matsayin gagarumar nasarar demokaradiyya mai sigar musamman ta yankin Hong Kong, sanarwar ta ce, zaben ya sake bayyana ingantaccen tsarin zabe da manufar al’ummar Hong Kong masu kishin kasa suke gudanar da harkokin yankinsu.(Ahmad)