logo

HAUSA

Yan bindiga sun kashe mutane sama da 20 a arewacin Najeriya

2021-12-20 09:44:43 CRI

‘Yan bindiga sun kashe mutane sama da 20 a hare haren da suka kai jihar Kaduna dake arewa maso yammacin Najeriya a ranar Asabar.

Samuel Aruwan, kwamishin al’amurran tsaron cikin gida na jihar Kaduna, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, an kaddamar da hare haren ne a kauyuka hudu dake karamar hukumar Gima, yayin da ‘yan ta’addan suka bude wuta kan mai uwa da wabi, tare da harbe mazauna kauyukan da kuma cinnawa gidaje wuta.

Aruwan ya ce, gwamnatin jihar ta ba da umarnin gaggawa na tantance wuraren da hare haren suka shafa domin samar da kayayyakin tallafin jin kai, sannan hukumomin tsaro za su ci gaba da zurfafa bincike a dukkan yankunan.

Hare haren ‘yan bindiga sun kasance a matsayin babbar barazanar tsaro dake damun yankin arewacin Najeriya, lamarin da ya yi sanadiyyar kashe rayuka da kuma yin garkuwa da mutane masu yawa musamman a watannin baya bayan nan.(Ahmad)