logo

HAUSA

Kungiyar OIC za ta kafa asusun agajin jin kai da shirin tallafin abinci ga al’ummar Afghanistan

2021-12-20 10:07:30 CRI

Kungiyar kasashe musulmi ta OIC, ta yanke shawarar kafa asusun agajin jin kai, da shirin tallafin abinci da saukaka bude hanyoyin hada-hadar kudi da na bankuna, domin tallafawa al’ummar Afghanistan dake fuskantar matsalar jin kai.

Ministan harkokin wajen Pakistan Shah Mahmood Qureshi ne ya bayyana hakan a jiya, yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da aka kira bayan taron koli karo na 17, na majalisar ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar da ya gudana a Islamabad. An kira taron ne domin tattauna yanayin da kasar ta Afghanistan ke ciki. A cewar Shah Qureshi, samun ci gaban tattalin arziki da taimakon jama’a ba yiwu ba tare da tsarin hada-hadar bankuna dake aiki yadda ya kamata ba.

Ya ce kungiyar OIC, ta kuma yanke shawarar tura manzon musammam zuwa Afghanistan, baya ga hada hannu tsakanin kungiyar da hukumomin MDD wajen kai kayayyakin agaji kasar.

Kimanin wakilai 70 daga kasashe mambobin kungiyar da wadanda ba na kungiyar ba da na hukumomin yanki da na kasa da kasa ne suka halarci taron. (Fa’iza Mustapha)