logo

HAUSA

Masu zanga-zanga a Sudan suna neman mulkin farar hula

2021-12-20 09:50:22 CRI

Dubban masu zanga-zanga ne suka kutsa shingen jami’an tsaro a Sudan, inda suka isa fadar shugaban kasar dake birnin Khartoum, suna neman mulkin farar hula. Lamarin wanda ya auku a jiya Lahadi, ya zo daidai da ranar da ake cika shekaru 3 da juyin juya halin kasar da ya kai ga hambarar da tsohon shugaba Omar al-Bashir.

Masu zanga-zangar sun bayyana adawarsu da yarjejeniyar siyasa da aka cimma tsakanin shugaban gwamnatin riko na kasar Abdel Fattah Al-Burhan da firaminista Abdallah Hamdok a ranar 21 ga watan Nuwamba.

Gammayar kungiyoyin al’umma dake rajin samar da ‘yanci da sauyi a kasar, sun yi kira da a ci gaba da nuna turjiya har sai an mika mulki ga farar hula.

Wani kwarya-kwaryan rahoto na kwamitin likitocin Sudan ya bayyana cewa, an kashe mutum guda cikin masu zanga-zangar yayin da wasu 80 suka jikkata.

Sudan dai na tsaka da fama da rikicin siyasa tun bayan da shugaban rundunar sojin kasar Abdel Fattah Burhan, ya ayyana dokar ta baci a ranar 25 ga watan Oktoba, inda kuma ya rushe gwamnatin riko na kasar. (Fa’iza Mustapha)