logo

HAUSA

Bankin duniya ya yaba da tallafin kasar Sin ga kasashe matalauta

2021-12-20 09:58:08 CRI

Bankin duniya ya yaba da tallafin kasar Sin ga kasashe matalauta_fororder_bankin duniya

Babban jami’in bankin duniya, Axel Van Trotsenburg, ya bayyana kasar Sin a matsayin wadda ke ci gaba da ba da gudunmuwa ga asusun bankin na IDA dake tallafawa kasashe matalauta, yana mai matukar jinjinawa kasar.

Axel Van Trotsenburg, wanda shi ne daraktan sashen kula da ayyuka na bankin, ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kasar Sin ta karbi tallafi daga asusun a shekarun 1980, kuma ta yi amfani da su ta hanyar da ta dace, inda ake cin ribarsu yanzu.

Asusun na IDA da aka kafa a shekarar 1960 na taimakawa kasashe matalauta ta hanyar samar musu da kudi da basussuka marasa kudin ruwa domin gudanar da ayyuka da shirye-shiryen bunkasa tattalin arzikinsu da yaki da fatara da inganta rayuwar jama’a.

A baya-bayan nan, bankin na duniya ya sanar da wani shirin asusun na dala biliyan 93, dake da nufin tallafawa kasashe 74 mafiya talauci a duniya. Shirin zai mayar da hankali ne kan farfado da kasashen daga mummunan tasirin COVID-19. (Fa’iza Mustapha)