logo

HAUSA

Qin Gang: ya kamata Sin da Amurka su yi kokari tare wajen tinkarar batutuwan duniya

2021-12-19 17:36:37 CRI

Jakadan kasar Sin dake kasar Amurka Qin Gang ya yi hira da Kim Montgomery, darektar sashen kula da harkokin kasa da kasa da kimiyyar diplomasiyya na mujallar Science & Diplomacy a ranar 17 ga wata, inda ya bayyana cewa, ya kamata Sin da Amurka su yi kokari tare don tinkarar batutuwan duniya, da daidaita barazanar da ake fuskanta sakamakon kirkiro sabbin fasahohi. Hadin gwiwarsu za ta taimaka wajen kawo moriya ga jama’ar kasashen biyu, kana za ta taimakawa dukkan dan Adam wajen samar da makoma mai kyau. Idan an kawo cikas ga hadin gwiwar, ciki har da daukar matakan kayyade masana da daliban kasar Sin dake kasar Amurka, hakan zai kawo illa ga moriyar kasashen 2 duka.

Qin Gang ya yi nuni da cewa, hadin gwiwar kimiyya da fasaha a tsakanin Sin da Amurka ta sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, muhimmin fannin ne na raya dangantakar dake tsakaninsu. A cikin shekaru fiye da 40 da suka gabata, bisa tsarin yarjejeniyar hadin gwiwar Sin da Amurka kan kimiyya da fasaha, kasashen 2 sun hada kansu a fannonin kiwon lafiya, da sauyin yanayi, da kiyaye muhalli, da tsaron nukiliya da sauransu.

Qin Gang ya kara da cewa, burin manufofin diplomasiyyar Sin a halin yanzu shi ne, tabbatar da zaman lafiya a duniya da sa kaimi ga ci gaban duk dan Adam da samun bunkasuwa tare. An fi maida hankali ga kimiyya da fasaha yayin da ake aiwatar da manufofin diplomasiyya. Alal misali, a fannin binciken sararin samaniya, Sin tana son yin hadin gwiwa tare da kasa da kasa bisa tushen girmama juna, da bude kofa ga waje da amincewa da juna, da kaucewa nuna bambanci ga juna, da samun daidaito da moriyar juna. Ya ce, sauyin yanayi shi ne kalubalen da dukkan dan Adam ke fuskanta tare, ana bukatar kasa da kasa su yi kokari tare wajen tinkararsa. Sin da Amurka suna da kyakkyawar makoma kan hadin gwiwarsu wajen tinkarar sauyin yanayi. (Zainab)