logo

HAUSA

Kakakin ma’aikatar wajen Sin: Ya kamata sojojin Amurka su amsa laifin kashe kashe a duniya

2021-12-18 18:01:33 CRI

Kakakin ma’aikatar wajen Sin: Ya kamata sojojin Amurka su amsa laifin kashe kashe a duniya_fororder_微信图片_20211218180111

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya sanar da cewa, ya kamata sojojin kasar Amurka su dauki alhakin laifukan yakin da suka aikata na kashe fararen hular da ba su aikata laifin komai ba a fadin duniya.

Wang Wenbin, ya yi wannan tsokaci ne a ranar Juma’a, a taron manema labarai da aka saba gudanarwa a kullum, yayin da yake maida martani kan matakin da hedkwatar tsaron Pentagon ta dauka na cewar babu wani jami’in soji da za ta hukunta bisa hannu a hare-hare ta jirage marasa matuka wanda ya kashe fararen hula goma a Kabul na kasar Afghanistan. Tsohon jami’in tattara bayanan sirri na hukumar sojojin Amurka wanda ya kalli yadda hare-haren suka faru, an yanke masa hukuncin zaman gidan yari na watanni 45 tun a farkon wannan shekarar, saboda bayyana asirin faruwar lamarin ga kafafen yada labarai.

Wang yace, wannan lamarin tamkar wasa da hankali ne ake yiwa al’umma game da abin da ake kira wai “demokaradiyya," "hakkin dan adam," da kuma "doka da oda" wanda Amurka ke ikirarin tabbatarwa.(Ahmad)