logo

HAUSA

Xi ya jaddada muhimmancin dunkulewar kasuwannin kasa da karfafa sanya ido ga ayyukan gwamnati

2021-12-18 18:03:23 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, a ranar Juma’a ya bukaci a kara azamar gina dunkulalliyar kasuwar kasa cikin hanzari, kana a karfafa ayyukan gwamnati wajen sanya ido.

Xi, ya kuma jaddada muhimmancin kara gina jami’o’i masu daraja ta farko a duniya da kuma fitattun fannonin nazari.

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da ya jagoranci taro na 23 na babbar hukumar zurfafa yin gyare-gyare ta kasar.(Ahmad)