logo

HAUSA

An shirya dandalin tattaunawa tsakanin masana da kwararru na kasashen Sin da Sudan ta Kudu

2021-12-18 17:25:29 CRI

An shirya dandalin tattaunawa tsakanin masana da kwararru na kasashen Sin da Sudan ta Kudu_fororder_src=http___06imgmini_eastday_com_mobile_20180905_20180905003430_2519d96f4f6f5c940b873a6b3a1ddf74_1_jpeg&refer=http___06imgmini_eastday

Jiya Jumma’a an gudanar da dandalin tattaunawa na masana da kwararrun kasashen Sin da Sudan ta Kudu, inda wakiliya ta musamman ta gwamnatin kasar Sin kan batutuwan Afirka Xu Jinghu, da jakadan Sin dake Sudan ta Kudu Hua Ning, da mataimakin ministan harkokin waje da hadin-gwiwar kasa da kasa na Sudan ta Kudu, Deng Dau Deng, suka halarci bikin bude taron. Wasu kwararru da masana na kasar Sin da kasar Sudan ta Kudu, gami da mataimakin wakilin musamman na sakatare-janar na MDD mai kula da harkokin Sudan ta Kudu, Mista Cong Guang, da wakilin hukumar shirin samar da abinci da aikin gona ta MDD wato FAO dake kasar, Mista Meshack Malo, sun yi musanyar ra’ayoyi dangane da batun hangen nesa kan hadin-gwiwar Sin da Sudan ta Kudu dake karkashin tsarin dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka wato FOCAC.

Mahalarta taron sun jinjinawa nasarorin da aka cimma a wajen taron ministoci karo na 8 na dandalin FOCAC wanda aka gudanar kwanan baya a Senegal, al’amarin da a cewarsu, ya kafa sabuwar alkibla da samar da sabbin damammaki ga hadin-gwiwar Sin da Afirka a sabon zamanin da muke ciki. Kwararru da masanan sun kuma bullo da muhimman shawarwari dangane da bangarorin hadin-gwiwar kasashen biyu a nan gaba.

A nasa bangaren, mista Deng Dau Deng, ya ce Sudan ta Kudu na fatan yin kokari tare da kasar Sin, don inganta mu’amala da hadin-gwiwa daga dukkan fannoni, da ciyar da dangantakarsu gaba. (Murtala Zhang)