logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Sin ya halarci taron majalisar bada shawara kan babban dandalin hadin-gwiwar kasa da kasa kan shawarar “ziri daya da hanya daya”

2021-12-18 17:21:43 CRI

Ministan harkokin wajen Sin ya halarci taron majalisar bada shawara kan babban dandalin hadin-gwiwar kasa da kasa kan shawarar “ziri daya da hanya daya”_fororder_W020211218060354144286

Jiya Jumma’a mamban majalisar gudanawar kasar Sin, wanda kuma shi ne ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya halarci taron shekara ta 2021 na majalisar bada shawara kan babban dandalin hadin-gwiwar kasa da kasa kan shawarar “ziri daya da hanya daya” ta kafar bidiyo.

Ministan Wang ya bayyana cewa, bana aka cika shekaru 8 da shugaba Xi Jinping ya bullo da muhimmiyar shawarar da ake kira “ziri daya da hanya daya”, ko kuma belt and road initiative a turance. A shekarun 8, an yi kokarin gudanar da ayyukan da suka shafi shawarar gami da cimma manyan nasarori.

Wang ya kara da cewa, tattalin arzikin duniya na cikin wani muhimmin lokaci yanzu na samun farfadowa. Kasarsa tana fatan yin kokari tare da abokan hadin-gwiwarta a fannoni hudu, wato, na farko, tsayawa haikan kan maida muradun al’umma a gaban kome. Na biyu, mutunta manufar hadin-gwiwa ta yin shawarwari da more damammaki tare. Na uku, nacewa ga bin hanyar hadin-gwiwa mai inganci. Na hudu, neman cimma burin samar da ci gaban duk duniya.(Murtala Zhang)