logo

HAUSA

An zartar da sanarwar Sharm El-Sheikh a taron MDD kan yaki da rashawa

2021-12-18 17:48:27 CRI

An zartar da sanarwar Sharm El-Sheikh a taron MDD kan yaki da rashawa_fororder_2e2eb9389b504fc268d141ed975a751892ef6dd9

A ranar Juma’a an kammala babban taron MDD kan yaki da rashawa a birnin Sharm El-Sheikh na kasar Masar, inda aka amince da sanarwar yaki da rashawa.

Sanarwar ta ce, taron ya zartar da yarjejeniyar Sharm El-Sheikh, da sauran batutuwa bakwai da aka amince da su, da kuma yarjejeniyar da aka cimma matsaya kanta game da kasar da zata karbi bakuncin taron karo na goma.

Sanarwar ta Sharm el-Sheikh, ta bayyana fargaba kan karuwar ayyukan rashawa dake faruwa ta hanyar kudaden da ake kashewa a ayyukan gaggawa ta fannonin raya tattalin arziki da tallafawa ayyukan kiwon lafiya, inda ta bukaci bangarorin da batun ya shafa da su tattaro ayyuka mafi inganci da aka gudanar da kuma kalubaloli, da nufin tsara wasu ka’idojin karfafa hadin gwiwa don yin kandagarki, da tantacewa, da yin bincike da kuma hukunta ayyukan rashawar da aka samu a lokutan gudanar da ayyukan jin kai na gaggawa, da kai dauki a yayin rikice-rikice.

Bugu da kari, bangarorin kasashe mahalarta taron sun amince Amurka ta karbi bakuncin taron karo na goma wanda zai gudana a shekarar 2023.(Ahmad)