logo

HAUSA

An kubutar da kananan yara 34 daga masu safarar yara a tsakiyar Najeriya

2021-12-18 16:02:36 CRI

Hukumomi a Najeriya sun ce a kalla yara 34 aka kubutar daga hannun masu safarar bil adama a yayin da jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasar NDLEA suka kai samame a babbar hanyar mota a jahar Kogi dake tsakiyar Najeriya.

Cikin wata sanarwar da kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar ya ce, yaran da lamarin ya shafa an gano su ne cikin motocin bas biyu, yayin da suke kan hanyarsu daga jahar Ogun dake shiyyar kudu maso yammacin kasar zuwa Abuja, babban birnin kasar.

A cewar Babafemi, kananan yaran, ‘yan tsakanin shekaru 8 zuwa 14, tun da farko an yi safararsu ne daga jahar Plateau dake shiyyar tsakiyar Najeriya zuwa jahar Ogun, daga nan kuma aka rarrabasu zuwa gidajen mutane daban daban a matsayin ‘yan aikin hidimomin gida.

Ya ce binciken da suka gudanar sun gano cewa, wasu daga cikin yaran sun yi ayyukan hidima na tsawon shekaru biyu ba tare da biyansu hakkoki ba.(Ahmad)