logo

HAUSA

Yawan yarjeniyoyin “ziri daya da hanya daya” da Sin ta sa hannu da kasashen waje sun zarce 200

2021-12-17 14:38:59 CRI

Yawan yarjeniyoyin “ziri daya da hanya daya” da Sin ta sa hannu da kasashen waje sun zarce 200_fororder_src=http___www.chinamil.com.cn_jwgz_attachement_jpg_site351_20170514_18037333a96f1a81ff1844&refer=http___www.chinamil.com

Mai magana da yawun hukuma mai kula da aikin gyare-gyare da raya kasa ta Sin Meng Wei, ta bayyana cewa, Sin ta kulla yarjeniyoyi karkarshin shawarar “ziri daya da hanya daya” da gwamnatocin Afrika ta tsakiya, da Guinea Bissau, da Eritrea, da Burkina Faso, da Sao Tome da Principe, da dai sauran kasashen Afrika da yawa. Kuma ya zuwa yanzu, Sin ta kulla irin wadannan yarjeniyoyi fiye da 200 da kasashe 145, da kungiyoyin kasa da kasa 32.

Madam Meng ta ce:

“A ranar 13 ga wata, an kira taro karon farko tsakanin Sin da AU, kan daidaita ayyukan dake shafar shawarar ‘ziri daya da hanya daya’, inda bangarorin biyu suka tattauna kan batun yakar COVID-19, da samar da hatsi, da makamashi, da zuba jari, da manyan ababen more rayuwa, da ma’aunin ingancin kayayyaki, da kuma yin kididdiga da sauransu, matakin da ya kara zurfafa hadin kansu.

Ban da wanann kuma, mahalarta taron sun sa hannu kan ‘takardar fahimtar juna, tsakanin hukumar yin gyare-gyare da raya kasa ta kasar Sin, da kwamitin AU, game da habaka hadin kan bangarorin 2 karkashin shawarar ziri daya da hanya daya’.”  (Amina Xu)