logo

HAUSA

An bukaci al’ummar Somaliya su goyi bayan kokarin tabbatar da zaman lafiyar kasar yayin da ake fama da kalubaloli

2021-12-16 10:16:00 CRI

Kwamandan Burundi mai barin gado na tawagar dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika a Somaliya (AMISOM), ya bukaci ‘yan kasar Somaliya da su goyi bayan kokarin tawagar don tabbatar da zaman lafiyar kasar yayin da ake fama da kalubaloli masu yawa.

Telesphore Barandereka, kwamandan Burundi mai barin gado na tawagar dakarun(AMISOM, ya bayyana cikin wata sanarwar da aka fitar a Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya cewa, wannan muhimmiyar dama ce da ya samu a matsayinsa na jami’in sojin Afrika wajen bayar da gudummawarsa don wanzar da zaman lafiya a kasar Somaliya, da shiyyar, da nahiyar Afrika, har ma ga zaman lafiyar duniya baki daya, sakamakon yadda ayyukan ta’addanci suka kara karade duk duniya. Jami’in ya bukaci ‘yan kasar Somaliya su goyi bayan kokarin da gwamnatin kasar ke yi da abokan hulda na kasa da kasa suke yi domin a samu nasarar maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.(Ahmad)

Ahmad