logo

HAUSA

Alkaluman FDI na kasar Sin ya karu da kashi 15.9% cikin watanni 11 na farkon bana

2021-12-16 21:13:54 CRI

Alkaluman FDI na kasar Sin ya karu da kashi 15.9% cikin watanni 11 na farkon bana_fororder_452400570522403052

Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta sanar Alhamis din nan cewa, jarin da ake zubawa kai tsaye daga wajen kasar Sin, ya karu da kashi 15.9 bisa 100 a watanni 11 na farkon shekarar bisa makamancin lokaci na bara, zuwa Yuan triliyan 1.04, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 157.2.