logo

HAUSA

An Kafa Tashar ’Yan Jaridu Ta CMG Dake Birnin Managua

2021-12-16 13:56:39 CRI

An Kafa Tashar ’Yan Jaridu Ta CMG Dake Birnin Managua_fororder_211216-Nicaragua-Maryam-hoto

Jiya Laraba, an kafa tashar ’yan jaridu ta Babban Gidan Rediyo da Talabijin na kasar Sin wato CMG dake birnin Managua, fadar mulkin kasar Nicaragua. Wannan shi ne tashar ’yan jaridu ta 190 da CMG ya kafa a kasashen ketare.

A yayin bikin bude tashar da aka yi a wannan rana, wakilan CMG da na kwamitin kula da kafar yada labarai na Nicaragua, da na kwamitin kula da harkokin jama’a sun kulla yarjejeniyar hadin gwiwa a hukumance, kuma, wannan shi ne yarjejeniya ta farko da kasashen Sin da Nicaragua suka kulla a fannin yada labarai bayan da suka farfado da huldar diflomasiyya a tsakaninsu.

Cikin jawabinsa, mai ba da shawara ga shugaban kasar Nicaragua, Laureano Ortega ya bayyana cewa, tashar da CMG ta kafa a kasarsa, za ta ba da taimako ga kasar Sin da ma sauran kasashen duniya wajen kara saninsu game da kasar Nicaragua, a sa’i daya kuma, za ta taimakawa jama’ar kasarsa wajen kara fahimtarsu game da kasar Sin.

Haka kuma, wakilin CMG, kana, shugaban tashar CMG dake Latin Amurka ya ce, tashar ’yan jaridun dake birnin Managua ta CMG za ta karfafa hadin gwiwa da mu’amalar dake tsakaninta da kafofin watsa labarai na kasar Nicaragua, domin karfafa ma’amalar dake tsakanin al’ummomin kasashen biyu, da kuma inganta hadin gwiwar kasashen biyu karkashin shawarar “Ziri daya da hanya daya”, ta yadda za a ba da gudummawar raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)