logo

HAUSA

Likitocin Sin sun yi wa takwarorin su na Kamaru karin haske game da fasahohin amfani da magungunan gargajiya

2021-12-16 10:46:57 CRI

Likitocin Sin sun yi wa takwarorin su na Kamaru karin haske game da fasahohin amfani da magungunan gargajiya_fororder_kamaru

Tawagar likitocin kasar Sin ta 21, wadda ke aiki a kasar Kamaru, ta shirya wani taron yini guda a jiya Laraba, domin horas da takwarorin su na Kamaru, game da ilmin likitancin gargajiyar kasar Sin.

An gudanar da taron ne a babban asibitin lura da mata da kananan yara dake birnin Yaounde, babban birnin kasar. Ya kuma hallara jami’an jinya da likitoci 50, yayin da kwararrun masana a fannin likitancin gargajiya 2 na Sin suka gabatar da jawabai.

Da yake tsokaci game da hakan, babban daraktan asibitin Robinson Mbu Enow, ya ce gwamnatin Kamaru na fatan samar da damammaki ga ‘yan Kamaru, dake fatan zuwa kasar Sin domin koyon karin ilmin likitancin gargajiyar kasar Sin.

A nasa jawabin kuwa, shugaban tawagar likitocin Sin dake Kamaru Tian Yuan, cewa ya yi horon na wannan karo, wani kokari ne da likitocin kasar Sin ke yi na yayata amfani da magungunan gargajiyar kasar Sin, domin inganta tsarin kiwon lafiya a Kamaru. (Saminu)

Saminu