logo

HAUSA

MDD: al'ummun Afghanistan na fuskantar matsalolin kare hakkin bil adama

2021-12-15 10:46:17 CMG

MDD: al'ummun Afghanistan na fuskantar matsalolin kare hakkin bil adama_fororder_211215-S1-Afghanistan

Mataimakiyar babban kwamishina mai lura da kare hakkin bil adama a MDD Nada Al-Nashif, ta ce dubban al’ummun kasar Afghanistan, na fuskantar matsaloli masu nasaba da kare hakkin dan adam.

Nada Al-Nashif, wadda ta bayyana hakan a jiya Talata, lokacin da yake tsokaci game da halin da ake ciki a Afghanistan, ta ce kasar wadda ta sha fama da tashe tashen hankula, na fama da tarin kalubale, ciki har da tasirin takunkumi da aka kakaba mata, da daskaras da kadarorin ta.

Al-Nashif ta fadawa zauren MDDr cewa, tun kafin ma kungiyar Taliban ta karbe iko da kasar a watan Agusta, a bana kasar ta samu adadi mafi yawa na fararen hula da suka rasa rayukan su, wadanda kusan rabin su mata ne da kananan yara.

Jami’ar ta ce, duk da an tsagaita yaki tun daga watan Agusta, har yanzu fararen hula a kasar na fuskantar tashe tashen hankula, yayin da kungiyar IS mai tunga a lardin Khorasan ke ci gaba da kaddamar da hare hare.

Al-Nashif ta hakaito wasu alkaluma da MDD ta fitar, dake nuna cewa, kaso 60 bisa dari na jimillar yaran Afghanistan miliyan 4 da dubu dari 2, da ba sa zuwa makaranta mata ne, kana wasu karin yaran miliyan 8 da dubu dari 8 na fuskantar barazanar rasa damar samun ilimi, sakamakon gaza biyan malamai albashi, da ci gaba da rufe wasu makarantun.  (Saminu)

Saminu