logo

HAUSA

Shugabannin kasashen Sin da Rasha sun gana ta kafar bidiyo

2021-12-15 21:06:00 cri

Shugabannin kasashen Sin da Rasha sun gana ta kafar bidiyo_fororder_1639573283(1)

A yammacin yau Talata ne, daga nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana ta kafar bidiyo da takwaransa na kasar Rasha Vładimir Putin.

A yayin ganawar, Xi Jinping ya nuna cewa, yana matukar farin cikin gudanar da taron bidiyo karo na biyu tare da shugaba Putin a karshen wannan shekarar, wannan ita ce ganawarsu ta 37 tun daga shekarar 2013.

Ya kara da cewa, a nan gaba kuma ya kamata bangarorin biyu su dage wajen yin musayar damammaki da juna, da ciyar da ajandar bunkasuwar duniya gaba.

Xi Jinping ya jaddada cewa, nan da fiye da wata guda, shugaba Putin zai ziyarci kasar Sin, tare da halartar bikin bude gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing, domin nuna goyon baya ga kasar Sin kan karbar bakuncin gasar. Ziyarar kuma za ta kasance ganawar ido da ido ta farko da shugabannin biyu za su yi a cikin shekaru biyu da suka gabata. Xi Jinping ya bayyana fatansa na yin mu'amala mai zurfi tare da shugaba Putin kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da manyan batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya, yana cike da imani kan cimma wasu sabbin muhimman ra’ayoyi.

Baya ga haka, bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayi kan alakar dake tsakanin manyan kasashen duniya da batun dimokaradiyya. Xi Jinping ya jaddada cewa, dimokuradiyya kyakkyawan fata ne na duk dan Adam, kuma hakki ne na al'ummar kasashen duniya baki daya. Ko wata kasa tana gudanar da tsarin dimokuradiyya da kuma yadda za ta inganta ta, al'ummarta ne kawai za su iya tantancewa. Ya kamata dukkan kasashen duniya su tattauna kan harkokin kasa da kasa, tabbatar da dimokuradiyyar dangantakar kasa da kasa da aiwatar da ra’ayin bangarori da dama na hakika, wannan shi ne abin da jama'a ke bukata bisa yanayin da ake ciki. Xi Jinping ya bayyana cewa, kasarsa a shirye take ta karfafa yin mu’amala da hadin kai tare da Rasha, da jagorantar al'ummomin duniya don kafa ra'ayin daidaito game da dimokaradiyya, da kare hakkin dimokaradiyya a dukkan kasashe.

A nasa bangare, shugaba Vładimir Putin ya bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen Rasha da Sin a halin yanzu, tana matsayi mafi kyau a tarihi, kuma ta amincewa da juna bisa manyan tsare-tsare, kana ta zama misali na samun moriyar juna da samun nasara tare bisa tushen rashin tsoma baki a cikin harkokin cikin gidan juna, da mutunta muradun juna, ana iya kiranta abin koyi na dangantakar kasa da kasa a karni na 21.

Putin ya ce, yana fatan ziyarar kasar Sin da sauri, tare da halartar bikin bude gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu na birnin Beijing. A cewarsa, kasar Rasha ko da yaushe tana adawa da yunkurin siyasantar da harkokin wasanni. Yana fatan yin musanyar ra'ayi sosai tare da shugaba Xi kan muhimman batutuwan dake jawo hankulansu duka, da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen Rasha da Sin. (Mai fassara: Bilkisu Xin)