logo

HAUSA

AU ta ce annobar COVID-19 ta baiwa duniya damar gina sabon tsarin kiwon lafiya don tinkarar matsalolin lafiya a nan gaba

2021-12-15 10:45:00 CMG

AU ta ce annobar COVID-19 ta baiwa duniya damar gina sabon tsarin kiwon lafiya don tinkarar matsalolin lafiya a nan gaba_fororder_211215-A1-AU

Kungiyar tarayyar Afrika AU ta bayyana cewa annobar COVID-19 da ake cigaba da fuskanta a halin yanzu ta samar da wata dama mai cike da tarihi don gina sabon tsarin kiwon lafiyar al’umma a Afrika domin tinkarar matsololin kiwon lafiya a nan gaba.

Moussa Faki Mahamat, shugaban gudanarwar kungiyar mai mambobin kasashen Afrika 55, yayi wannan tsokaci ne a wajen kaddamar taron kasa da kasa kan batun kiwon lafiyar Afrika wato (CPHIA-2021), wanda ke gudana tsakanin 14 zuwa 16 ga watan Disamba ta kafar bidiyo.

Mahamat ya jaddada cewa, ana fatan taron zai samar da muhimmin dandali wanda zai tattaro zukata masu tunani da hangen nesa wajen nazartar fannin kiwon lafiyar al’ummar Afrika don cimma wannan muhimmin buri.

Ana sa ran taron na kwanaki uku, zai samu mahalarta sama da 10,000 daga kasashen duniya 140, don gabatar da jawabai daga shugabannin kasashe da gwamnatocin kasashen Afrika, da muhimman mutane da kwararrun masana kiwon lafiya.

Ana fatan mahalartan zasu tattauna nasarorin da aka samu cikin hanzari game da yaki da annobar COVID-19 da kuma gabatar da sabbin hanyoyin inganta fannin kiwon lafiyar jama’a a nahiyar.

A cewar hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika CDC, taron CPHIA-2021 ya zo a lokacin da Afrika da duniya ke cikin mawuyacin hali.(Ahmad)

Ahmad