logo

HAUSA

Sin za ta taimakawa jama’ar kasar Afghanistan wajen daidaita matsalarsu

2021-12-15 11:01:57 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labarai da aka gudanar a jiya cewa, Sin za ta ci gaba da samar da gudummawar jin kai cikin gaggawa ga kasar Afghanistan, don taimakawa jama’ar kasar wajen daidaita matsalarsu.

A ranar 12 ga wannan wata, an yi bikin aza tubalin gina rijiyoyin ruwa da ofishin jakadancin Sin dake kasar Afghanistan ya taimakawa gwamnatin wucin gadi ta kasar samarwa. Kaza lika a ranar 13 ga wannan wata, aka yi bikin mika kayayyakin jin kai da gwamnatin kasar Sin ta samarwa Afghanistan a karo na biyu a birnin Kabul.

Wang Wenbin ya yi bayanin cewa, a matsayin kasa mai makwaftaka da Afghanistan kuma abokiyarta, Sin na samar da goyon baya ga Afghanistan a fannin shimfida zaman lafiya da bunkasa tattalin arziki. Ayyukan kyautata zaman rayuwar jama’a da kasar Sin ta taimakawa Afghanistan samarwa, za su saukakawa jama’ar kasar biyan bukatunsu na amfani da ruwa, da kuma kyautata zaman rayuwarsu. (Zainab)