logo

HAUSA

Kasar Sin ta yaba da goyon bayan da ake baiwa wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing

2021-12-14 20:29:07 CRI

Kasar Sin ta yaba da goyon bayan da ake baiwa wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing_fororder_W020211214217261105104

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana jin dadin kasarsa kan goyon bayan da kasashen da abin ya shafa, da kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na duniya suka nunawa gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing da kuma matsayinsu na adawa da siyasantar da harkokin wasanni.

A baya-bayan nan ne wasu shugabanni da manyan jami'ai daga kasashe da dama, da suka hada da Venezuela da Cuba, sun bayyana matsayinsu na cewa, bai kamata a rika siyasantar da wasannin Olympics ba, kuma suna goyon bayan wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing. Sanarwar taron koli na Olympics karo na 10, ita ma ta nuna adawa da siyasantar da wasannin Olympics da ma wasanni gaba daya.

Wang ya kuma lura da cewa, kundin tsarin wasannin Olympic ya bayyana karara cewa, gudanar da wasannin motsa jiki, hakki ne na dan Adam . A don haka ya ce, sanya siyasa a gasar wasannin Olympic, ba kawai cin zarafin 'yan wasa ba ne, har ma yin Allah wadai ne da ruhin Olympics, wanda ya sabawa yanayin da ake ciki na rungumar hadin kai.