logo

HAUSA

An isar da wasu karin alluran rigakafin COVID-19 da Sin ta samar birnin Yamai

2021-12-14 13:51:09 CRI

An isar da wasu karin alluran rigakafin COVID-19 da Sin ta samar birnin Yamai_fororder_1

A jiya Litinin ne an isar da wasu karin alluran rigakafin COVID-19 da gwamnatin Sin ta samarwa jamhuriyar Nijar a birnin Yamai, hedkwatar kasar, inda jakadan Sin dake Nijar Jiang Feng, da ministan kiwon lafiya na kasar Illiassou Mainassara, sun halarci bikin karbar alluran.

Da yake tsokaci yayin tarbar rigakafin, jakada Jiang Feng ya nuna cewa, Sin sahihiyar abokiya ce ga kasashe masu tasowa, tana kuma dukufa wajen samarwa kasashe masu tasowa isassun allurai. Ya ce Sin ta yanke shawarar samarwa kasar alluran ne a sabon zagaye kyauta, don taimaka mata wajen tinkarar cutar. Ban da wannan kuma, tana kokarin hadin kai da Nijar, wajen kafa kyakkyawar makomar kasashen biyu, da bangaren Sin da Afrika a fannin kiwon lafiya.

A nasa bangare, a madadin shugaban kasar Mohamed Bazoum, Illiassou Mainassara, ya jinjinawa hadin kan Sin da Nijar. Ya ce, gwamnatin kasar da jama’ar ta, suna matukar godiya bisa taimakon da Sin ta baiwa kasar a wannan karo, matakin da zai inganta karfin kasar na yiwa jama’a alluran. Nijar dai na fatan kara yin hadin kai da kasar Sin a fannin kiwon lafiya, ta yadda za a ingiza bunkasuwar dangantakar kasashen biyu zuwa wani sabon matayi. (Amina Xu)