logo

HAUSA

An gudanar da bikin tunawa da kisan kiyashin da mahara Japanawa suka yi a birnin Nanjing

2021-12-13 14:00:53 CRI

An gudanar da bikin tunawa da kisan kiyashin da mahara Japanawa suka yi a birnin Nanjing_fororder_1213-Nanjing-Saminu

A yau Litinin 13 ga wata ne ake cika shekaru 84, tun bayan da mahara Japanawa suka mamaye birnin Nanjing, tare da aiwatar da kisan kiyashi kan al’ummar birnin cikin tsawon makwanni 6, da nufin kawo karshen jama’ar birnin baki daya. An tabbatar da yiwa sama da Sinawa 300,000 yankan rago a yayin harin na Japanawa, lamarin da ya kasance mummunan abun bakin ciki a tarihin bil adama.

Domin tunawa da wannan lamari, an gudanar da bikin kasa na tunawa da wadanda suka rasa rayukansu a birnin na Nanjing da sanyin safiyar Litinin din nan, bikin da ya samu halartar kusan wakilai 3,000 daga sassan rayuwa daban daban.   (Saminu)