logo

HAUSA

Sassan jam’iyyu da kungiyoyin al’umma sun fitar da takardar hadin gwiwa game da matsayar su don gane da dimokaradiyya

2021-12-13 14:35:05 CMG

Sassan jam’iyyu da kungiyoyin al’umma sun fitar da takardar hadin gwiwa game da matsayar su don gane da dimokaradiyya_fororder_1213-dimokuradiyya

A yau Litinin ne sassan jam’iyyun siyasa, da kungiyoyin al’umma, da kwararru sama da 355 daga kasashe da yankuna 140, suka zanta da ofishin tuntuba na kwamitin tsakiyar JKS ta hanyoyi daban daban, kana suka fitar da wata takardar hadin gwiwa bisa radin kan su, game da matsayin su don gane da dimokaradiyya.

Takardar sanarwar dai ta bayyana yadda ya kamata kasashe da yankuna, su zabi salon dimokaradiyya da ya dace da su, tare da yin aiki tare, don bunkasa ci gaban bil adama na bai daya. Takardar ta kuma jaddada cewa, dimokaradiyya nasara ce da dan adam baki daya ya cimma a fagen siayasar zamani. Kuma ci gaban rayuwa babban buri ne na daukacin bil adama.

Bugu da kari, takardar ta bayyana cewa, ba wani tsarin dimokaradiyya kwaya daya, wanda zai dace da dukkanin kasashe ko yankuna. Don haka sassan da suka fitar da takardar, suke adawa da tsoka bakin wata kasa cikin harkokin gidan saura da sunan kare dimokaradiyya, suna masu kira da a martaba ka’idojin bai daya na inganta rayuwar al’ummar duniya, ta yadda za a kai ga cimma nasarar kafa al’ummar duniya mai makomar bai daya.  (Saminu)

Saminu