logo

HAUSA

Kasar Sin na adawa da lahanta moriyarta da kungiyar G7 ke yi

2021-12-13 20:14:40 cri

Kasar Sin na adawa da lahanta moriyarta da kungiyar G7 ke yi_fororder_src=http___imagecloud.thepaper.cn_thepaper_image_168_975_746&refer=http___imagecloud.thepaper

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a yau Litinin cewa, kasarsa na adawa da yadda G7 take tsoma baki a harkokin cikin gidanta, da bata sunan kasar, da ma cutar da muradun kasar Sin.

Rahotanni sun bayyana cewa, sakatariyar harkokin wajen Birtaniya Elizabeth Truss ta fitar da sanarwar kasar dake shugabancin taron ministocin harkokin wajen kasashen G7, inda ta bayyana cewa, dukkan bangarorin sun tattauna batutuwa da dama da suka shafi kasar Sin, ciki har da zaman lafiyar Hong Kong, da Xinjiang, da tekun gabashi da na kudancin kasar Sin, da kuma mashigin tekun Taiwan da sauransu.

Game da haka, Wang ya bayyana cewa, matsayin kasar Sin kan wadannan batutuwan bai sauya ba. Ya kara da cewa, jimillar al'ummar Amurka da Biritaniya ta kai kusan kashi 5% na al'ummar duniya, kuma su ne kasashe mafi ci gaban tattalin arziki da fasahar likitanci a duniya, sai dai masu kamuwa da cutar COVID-19 da kuma wadanda ke mutuwa sakamakon cutar ya kai kusan kashi 23% da 18% na duniya baki daya. A don haka, ya kamata, Amurka da Biritaniya da sauran wasu kasashe, su kare hakkin jama’arsu na rayuwa da lafiya, tare da yin aiki tukuru don hana karin asarar rayukan jama’a sakamakon annobar, maimakon maganar dimokuradiyya da ‘yancin dan Adam marasa tushe. (Bilkisu Xin)