logo

HAUSA

Gwamnatin kasar Amurka ta taba sa ido kan ‘yan jaridan kasar bisa dalilin yaki da ta’addanci

2021-12-13 11:40:17 CRI

Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Amurka wato AP ya bayar a kwanakin baya, an ce, wani rukunin musamman dake karkashin jagorancin hukumar kwastan da tabbatar da tsaro a iyakar kasa ta kasar Amurka, ya taba yin amfani da tsarin sako na gwamnatin kasar don sa ido kan ‘yan jarida, ko da yake an kafa wannan tsari domin neman dakile ‘yan ta’adda.

Wani ma’aikaci dake aiki a hukumar ya bayyana cewa, ya taba shiga aikin sa ido kan ‘yan jarida a shekarar 2017. Ya ce wannan aiki ne da ake gudanarwa a yau da kullum.

Kamfanin AP ya bayar da sanarwa game da wannan batu, inda ya yi Allah wadai da aikin sa ido kan ‘yan jarida, yana mai cewa aiki ne da ake gudanar da shi bisa yin amfani da ikon gwamnati fiye da kima, ba tare da bin doka ba. (Zainab)