logo

HAUSA

Yawan wutar lantarki da aka samar ta na’urorin samar da wutar lantarki ta karfin iska da hasken rana na kasar Sin ya kai matsayin farko a duniya

2021-12-13 11:46:25 CRI

Yawan wutar lantarki da aka samar ta na’urorin samar da wutar lantarki ta karfin iska da hasken rana na kasar Sin ya kai matsayin farko a duniya_fororder_1213-02

A gun taron kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta Sin kan ayyukan tattalin arziki da aka gudanar a kwanakin baya, an jaddada cewa, cimma burin yawan sinadarin cabon da ake fitarwa da yawansu zai kai matsayin koli, kana ya fara raguwa, tare da daidaita yawan gurbatacciyar iska da ake fitarwa, ta hanyoyin shuka itatuwa, da rage fitar da gurbatacciyar iska da sauransu, shi ne bukatun cikin gida na kasar Sin yayin da ake sa kaimi ga samun bunkasuwa mai inganci.

A yankin teku dake birnin Yancheng na lardin Jiangsu, akwai wani wuri dake kunshe da na’urorin samar da wutar lantarki ta karfin iska da hasken rana a kan teku mafi girma a kasar Sin, kuma ya zuwa karshen shekarar bana, za a fitar da wutar lantarkin da aka samar daga wurin zuwa dukkan sassan kasar Sin, inda yawan wutar lantarkin da za a rika samar da ita a kowace shekara zai kai kilowatt biliyan 17.3 a kowace awa. An ce yawansu zai kai kimanin rabin wutar lantarkin da ake bukatar a birnin Yancheng.

Ya zuwa karshen watan Nuwanba, yawan wutar lantarkin da aka samar ta hanyar makamashi masu tsabta a birnin Yancheng, ya kai kashi 67 cikin dari bisa jimillarsu, wanda ya kai matsayin farko a yankin gabashin kasar Sin.

Bugu da kari, ya zuwa karshen watan Oktoba, yawan wutar lantarki da aka samar ta na’urorin samar da wutar lantarki ta karfin iska na kasar Sin, ya kai kilowatt miliyan 300, wanda ya karu da kashi 30.4 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. Kana yawan wutar lantarki da aka samar ta hasken rana ya kai kilowatt miliyan 280, adadin da ya karu da kashi 23.7 cikin dari, don haka yawan wutar lantarki da aka samar ta na’urorin yin amfani da karfin iska da hasken rana na kasar Sin, ya kai matsayin farko a duniya. (Zainab)