logo

HAUSA

An bude taron karawa juna sani na hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin kere-kere

2021-12-13 09:38:07 CRI

An bude taron karawa juna sani na hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin kere-kere_fororder_1213-innovation-Saminu

A jiya Lahadi ne aka bude taron karawa juna sani, na hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka a fannin kere-kere, a birnin Wuhan fadar mulkin lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin.

Taron na bana na yini biyu, ya karkata ne ga aiwatar da shawarar nan ta “ziri daya da hanya daya”, da bunkasa manufar gina al’ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya.

An gudanar da ayyuka da dama ta yanar gizo da kuma a zahiri, ciki har da dandaloli daban daban, da baje kolin nasarorin da aka cimma karkashin hadin gwiwar sassan biyu a fannin kere-kere, da nune nunen fasahohin matasan Afirka a fannin kira da raya sana’o’i.

A yayin bikin bude taron, an sanya hannu kan takardun amincewa da wasu ayyukan hadin gwiwa 15, na kimiyya da fasaha karkashin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka da dama.

Taron ya kuma gudana ne karkashin jagorancin ma’aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin, da hadin gwiwar gwamnatin lardin Hubei. Kaza lika bikin bude taron ya samu halartar wakilai daga kasashen Afirka sama da 20, da kuma wasu matasan nahiyar, da masu bincike, da dalibai dake birnin na Wuhan.   (Saminu)