logo

HAUSA

Mutane 84 sun mutu sakamakon mummunar iska da ta ratsa jahohin Amurka

2021-12-12 17:24:39 CRI

Mutane 84 sun mutu sakamakon mummunar iska da ta ratsa jahohin Amurka_fororder_d009b3de9c82d158bab63d6fd15189d1bd3e4298

A kalla mutane 84 ne ake kyautata zaton sun mutu bayan da wata mahaukaciyar iska mai karfin gaske ta ratsa wasu jahohin Amurka da dama da tsakar dare, kamar yadda jami’ai suka bayyana.

Ita dai wannan iska mai karfi, ta rushe wani ginin kamfanin samar da fitilar kyandir dake birnin Mayfield, a jahar Kentucky, a daidai lokacin mutane kusan 110 ne ke cikin ginin, kamar yadda gwamnan jahar Andy Beshear, ya fadawa manema labarai a ranar Asabar.

Wasu hotuna daga garin Mayfield sun nuna yadda wasu gine-gine suka fada kan titinan mota, yayin da iskar ta tumbuke bishiyoyin da fala-falan wutar lantarki inda wayoyin lantarkin suka zube kasa.

A kalla mutane shida ne suka mutu a wani katafaren gini na kamfanin Amazon dake jahar Illinois bayan da iskar ta ratsa ta yankin a daren Juma’a, kamar yadda gwamnan jahar J.B. Pritzker ya bayyana

Haka zalika, a jahohin Arkansas, Missouri, da Tennessee an samu rahoton hasarar rayuka dake da nasaba da mahaukaciyar guguwar, inda jimillar adadinsu ya kai mutane takwas.

A yayin gabatar da bayanan gargadi game da yiwuwar faruwar iskar da safiyar ranar Juma’a, hukumar hasashen yanayi ta kasar ta sanar da cewa, akalla mutane kusan miliyan 25 suke cikin barazanar fuskantar mummunar iskar da zata ratsa shiyyar.(Ahmad)