logo

HAUSA

Jakadan kasar Sin dake Najeriya ya gana da ministan lafiyar Najeriya

2021-12-12 16:43:45 cri

Jakadan kasar Sin dake Najeriya ya gana da ministan lafiyar Najeriya_fororder_微信图片_20211212164315

A ranar 10 ga watan Disamba, jakadan kasar Sin dake Najeriya Cui Jianchun, ya gana da ministan lafiya na Najeriya Osagie Ehanire.
A yayin ganawar, jakada Cui ya bayyana cewa, kasashen Sin da Najeriya na taimakawa juna a yaki da annobar COVID-19 cikin hadin gwiwa, wannan ya nuna babban matsayin dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu. An kammala taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka na sabon zagaye cikin nasara, inda "Ayyuka 9" game da hadin kai a tsakanin bangarorin biyu da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar, sun ba da fifiko kan aikin kiwon lafiya, wanda ya samu karbuwa daga bangarori daban daban. Jakadan ya kara da cewa, kasar Sin tana son yin kokari tare da kasar Najeriya don tabbatar da nasarorin da aka cimma a wajen taron, da inganta matsayin hadin gwiwa a fannin yaki da annobar, da kuma sa kaimi ga ayyukan hadin gwiwar kiwon lafiya masu amfanawa jama’a irin na samun moriyar juna, ta yadda za a ba da gudummawa wajen gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afirka a zabon zamani.
A nasa bangaren, minista Ehanire ya bayyana cewa, kasashen Najeriya da Sin suna da kyakkyawar dangantaka, kana suna gudanar da hadin gwiwar kut-da-kut, kasarsa tana godiya ga kasar Sin sakamakon taimakon da ta bayar na samar da kayan aiki, da more fasahohin da ta samu wajen yaki da annobar COVID-19, hakan ya taimakawa kasar Najeriya wajen shawo kan wannan mawuyacin lokaci na tinkarar annobar. A cewarsa, sabbin matakai da alkawurran hada kai da Afirka da shugaba Xi ya bayyana a sabon taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka suna karfafawa al’umma gwiwa. Bangaren Najeriya yana son karfafa yin mu’amala tare da kasar Sin, da zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannonin hadin gwiwar samar da alluran rigakafin COVID-19, da kayayyakin more rayuwa ta fuskar kiwon lafiya, da musayar fasahohin da suka samu wajen gudanar da ayyukan kiwon lafiya da dai sauransu, ta yadda za a kara samar da alherai ga jama’ar kasashen biyu. (Bilkisu)