logo

HAUSA

Taron koli na Olympics: Ana adawa da duk wani yunkurin siyasantar da wasannin Olympics da wasan motsa jiki

2021-12-12 17:09:55 cri

Taron koli na Olympics: Ana adawa da duk wani yunkurin siyasantar da wasannin Olympics da wasan motsa jiki_fororder_641 (1)

A ranar 11 ga watan Disamba ne aka kammala taron koli na Olympics karo na 10. Sanarwar taron da kwamitin shirya wasannin Olympics na kasa da kasa ya fitar a shafinsa na yanar gizo ya bayyana cewa, taron ya yi kakkausar suka ga duk wani yunkurin siyasantar da wasannin Olympics da wasan motsa jiki, kana ta jaddada cewa, wajibi ne kwamitin Olympics na kasa da kasa, da wasannin Olympics da ma daukacin wasan Olympics su kiyaye matsayinsu na ‘yan ba ruwanmu a fannin siyasa.

Sanarwar taron ta kuma bayyana cewa, mahalarta taron sun fahimci shirye-shiryen karshe na wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing na shekarar 2022, ciki har da yadda aka samu nasarar gudanar da jerin gasa na gwaji. Gasar Olympics din ta Beijing za ta zama farkon sabon zamanin wasannin hunturu na duk duniya. Babban taron MDD karo na 76, ya amince da kudurin shawarwarin sulhu na gasar Olympics da kasar Sin da kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa suka tsara tare, wanda kasashe mambobi 173 suka gabatar. Mahalarta taron kolin sun yi marhabin da gagarumin goyon bayan da kasashe mambobin MDD ke ba wa gasar Olympics. (Bilkisu)